1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

'Yan sanda sun murkushe masu bore a Santanbul da Paris

May 1, 2024

'Yan sandan Turkiyya sun harba hayaki mai sa hawaye da harba harsashen roba ga dubban masu zanga-zangar ranar daya ga watan Mayu tare kuma da cafke mutane sama da 200.

https://p.dw.com/p/4fPIE
Masu zanga-zanga a birnin Istanbul na kasar Turkiyya
Masu zanga-zanga a birnin Istanbul na kasar TurkiyyaHoto: Khalil Hamra/AP Photo/picture alliance

Dubun dubatar mutane sun fantsama kan tituna a sassa daban-daban na duniya domin gudanar da zanga-zangar adawa da yadda ake tafiyar da al'amuran da suka shafi rayuwar ma'aitaka.

Karin bayani: An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Gaza a Turkiyya

Baya ga cafke mutane sama da 210 a dandalin Taksim na birnin Santanbul, 'yan sandan birnin Paris na kasar Faransa sun cafke mutane 25 a ke gudanar da boren karancin albashi da kuma bukatar dakatar da yakin Gaza.

Karin bayani: 'Yan kabilar Uighur na zanga-zanga a Turkiyya 

A nan Jamus mutane 10 ne suka samu raunuka sakamakon arangama da sukayi a lokacin rangadin ranar ma'aikata a birnin Freiburg da ke kudu maso yammacin kasar ta Jamus.