1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: NLC ta yi watsi da karin albashi

Uwais Abubakar Idris
May 1, 2024

Kungiyara kwadagon Najeriya NLC ta yi watsi da karin albashi na kashi 35 cikin 100 da gwamnatin ta sanar a dai dai lokacin da ma'aikatan ke bikin ranar ma'aikata ta duniya

https://p.dw.com/p/4fP3t
'Yan kungiyar kwandagon Najeriya
'Yan kungiyar kwandagon NajeriyaHoto: Uwais/DW

Kungiyara kwadagon Najeriya ta NLC ta yi watsi dsa Karin al;bashi na kasha 35 cikin 100 da gwamnatin ta sanar a dai dai lokacin da ma'aikatan ke bikin ranar ma'aikata  ta duniya, kungiyar ta ce suna juyayin halin da ma'aikatan Najeriyar suka samu kiansu a ciki na matsin rayuwa. 

Karin BayaniNajeriya: Kungiyar NLC ta yi watsi da karin farashin mai

'Yan kungiyar kwandagon Najeriya
'Yan kungiyar kwandagon NajeriyaHoto: Uwais/DW

Gwamnatin dai ta sanar da karin albashin ne a jajiberen ranar ma'aikata da ake yi a ranar 1 ga watan mayu. Karin albashin ya nuna kashi 25 zuwa kashi 35 cikin dari ga rukunoni shida na ma'aikatan, kuma ya shafi daukacin albashin da ma'aikatan ke karba ba wai mafi kankantar da aka saba kari a kansa ba. Mallam Abdulazi Abdulazi mai baiwa shugaban Najeriyar shawara a fanin yada labaru ya ce cika alkawari ne da karimci irin na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Karin Bayani: Albashi ya gagari wasu gwamnoni a Najeriya

Tuni ma'aikatan gwamnatin a Najeriyar da suka kosa da jin wani labari na karin albashin suka fara murnar kai wa ga haka, domin an kwashe lokaci mai tsawo ana tattaunawa a kan wannan batu na karin albashi saboda tsadara rayuwa da ta jefa su a ciki. 

'Yan kungiyar kwandagon Najeriya
'Yan kungiyar kwandagon NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Sai dai kasa da sao'i 24 da sanar da karin albashin da gwamnatin ta yi, 'yan kwadagon a karkashin kungyarsu ta NLC suka sa kafa suka yi fatali da karin albashin, suna cewa basu yarda ba domin ba haka suka yi da gwamnatin ba. 

Karin Bayani: Najeriya za ta kara wa ma'aikata albashi

Ma'aikatan gwamnatin Najeriyar dai na cikin wadanda ke da albashi mafi kankanta idan aka kwatanata su da na sauran kasashen duniya. Wani bincike da bankin raya kasashe Afrika ya gudanar ya nuna cewa kashi 34.4 na ma'aikatan Najeriya dukkaninsu matalauta ne saboda rashin isasshen albashi.