1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ma'aikata na fuskantar wahaloli a duniya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 1, 2024

A albarkacin ranar ma'aikata ta duniya Najeriya ta yi karin kudin albashi mafi karanci.

https://p.dw.com/p/4fNsx
Hoto: Jean-Marc Wiesner/Geisler-Fotopress/picture alliance

A Kasashe da da dama an kaddamar da bikin na ranar ma'ikatan ne cikin hali na karancin kudi da tsadar rayuwa. Gwamnatin tarayyar Najeria ta sanar da karin albashin ma'aikata da kashi 25 da kuma kashi 35 cikin 100, wanda zai yi waiwayen komawa tun watan Janairun da ya gabata don fara cin gajiyarsa, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke fuskantar tsananin rayuwa mafi muni a cikin shekaru 30.

Karin bayani:Najeriya: Karancin man fetur na kara tsanani

Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar kula da albashin kasar ta fitar, tana mai cewa karin albashin ya shafi dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya, da suka hada da jami'an tsaro da na lafiya da kuma na ilimi.

Karin bayani:Najeriya za ta kara wa ma'aikata albashi

Mafi karancin albashin ma'aikata a duk wata ya kama naira 37,500, a shekara kuma naira 450,00 daidai da Dalar Amurka 323.97.

Karin bayani:Najeriya: Kara karfin aljihun 'yan siyasa

Hauhawar farashi a Najeriya ya kai kashi 33.20 cikin 100, kuma shi ne mafi tsanani a cikin shekaru 28, bayan da gwamnatin kasar ta janye tallafin man fetur da kuma yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa kasa wanwar.